Ta faru: Bam ya tashi yayin da jama'a ke tsakar kwankwadar barasa a jihar Taraba, da dama sun jikkata


Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da tashin bam a wani wurin sha da ke Jalingo babban birnin jihar. 

 Kakakin rundunar, Abdullahi Usman, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne a Jika Doruwa, cikin babban birnin Jalingo a daren Lahadi, 14 ga Mayu, 2023. 

 Hukumar ta PPRO, wadda ba ta iya tantance adadin wadanda suka mutu har zuwa lokacin da aka buga wannan rahoto, ta ce an tura rundunar da ke yaki da bama-bamai a yankin domin sanin irin barnar da fashewar ta yi.

 Fashewar wadda aka ce ta auku ne da misalin karfe 9 na dare, an ce ta yi sanadiyyar jikkata wasu da dama, wadanda akasarinsu na jinya a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke FMC a Jalingo.

 Wata shaidar gani da ido da ta bayyana sunanta Peace Danjuma, wadda ta yi ikirarin cewa daya daga cikin kawayenta ya samu raunuka, ta ce fashewar ta zo masu a bazata, inda lamarin ya faru kwatsam.

 “Muna a wata unguwar da ake kira Jika, sai wani abu a karkashin kujera da muke zaune ya fashe,” inji ta.

 Har yanzu dai hukumomin kasar ba su fitar da adadin wadanda suka jikkata a lamarin ba har ya zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN