Ku yi shirin fuskantar kalubalan rayuwa bayan kun bar mulki, Saraki, tsoffin Gwamnoni sun shawarci Gwamnoni masu barin mulki


An tunatar da gwamnoni masu shigowa da masu barin gado cewa mulki na wucin gadi ne.

 An bukace su da su kasance masu tawali’u sa’ad da suke shirin rayuwa bayan kammala aikin ofishin gwamna, wanda ke da Ć™alubalensa.

 Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma gwamnan Kwara, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, sun bayyana abubuwan da suka faru a rayuwarsu bayan kammala aikin gwamnati.

 Takwarorinsu na jihohin Neja da Gombe, Muazu Babangida Aliyu da Ibrahim Dankwambo, sun ce idan aka yi kyakkyawan shiri, sakamakon lamarin zai zo da sauki.

 Sun bukaci sababbin gwamnoni da su tsara yadda za su fita daga farkon ranar da suka karbi mulki, domin kada su sha mamaki, idan wa’adinsu na mulki ya kare.

 Tsoffin gwamnonin sun yi magana ne a daren Lahadi a wani liyafar cin abincin bankwana da kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta gudanar a Abuja ga gwamnoni masu barin gado.

 Saraki wanda ya kasance gwamna na wa’adi biyu kuma tsohon shugaban NGF, ya tunatar da gwamnonin masu barin gado cewa abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke ba a lokacin da suke mulki, ya kuma gargade su da yin katsalandan a cikin harkokin magajin ba tare da an gayyace su ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN