Wata budurwa mai suna Ameerah ta rasu makonni biyu kafin ranar daurin aurenta a garin Ayagi dake karamar hukumar Dala a jihar Kano.
Umar Habib Sadiq Ayagi, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Lahadi, 14 ga Mayu, 2023.
Shi ma shugaban kungiyar daliban hadin gwiwa ta jihar Kano (COSA) Kwamared Abdullahi Dan Bording ya tabbatar da wannan labari mai ban tausayi a ranar Litinin.
BY isyaku.com