Siyasar Kano: Abubuwa 2 Rak Za Su Hana Abba Kabir Yusuf Zama Gwamnan jihar Kano – Jagoran APC


Ahmadu Haruna Dan Zago wanda yana cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Kano, ya fadakar da mutanensa da cewa su zama wayayyu. Legit Hausa ya wallafa.

A wata zantawa da ya yi da gidan rediyon Nasara FM, ‘dan siyasar ya ce yaudarar kai ne kurum a rika tunanin APC za ta zarce a kan mulki a Kano.

Ambasada Ahmadu Haruna Dan Zago ya nuna babu ta yadda za a fasa rantsar da Abba Kabir Yusuf, a nada Nasiru Yusuf Gawuna a madadinsa.

A matsayinsa na gogagge, Dan Zago ya ce ana neman maida ‘ya ‘yan APC jahilai, wawaye ko dakikai, har ma yana neman zama masu abin kunya

Jagoran na APC yake cewa dokar kasar nan da tsarin mulki sun ce bayan kwanaki bakwai da ayyana zabe, duk wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu.

An rahoto Dan Zago yana cewa in dai ba kotun koli ta ruguza nasarar jam’iyyar NNPP, babu yadda za a warware rantsar da Abba Kabir Yusuf da za ayi.

Me zai hana rantsar da Abba?

Tun da an yi zabe, kuma an bada takardar shaidar nasara, ana jiran rantsuwa, mu na da hankali, mu ba jahilai ba ne.

Abin da za su hana a rantsar da Abba a Kano; Ko dai ya mutu ko kuma an yi juyin mulki a Najeriya.

Idan Allah ya karbi kwanansa, dama ‘Dan Adam ne shi kuma duk mai rai mamaci. Ko kuma juyin mulki aka yi a Najeriya, aka jingine tsarin mulkin.

Amma ina tabbatar maka ba a yin Kantoma a gwamna. Sai dai idan an kafa gwamnatin riko na gaggawa, ita ma watanni shida ta ke ciki.

Amma idan an yi zabe babu wata karya da za ayi wa mutane cewa ba za a rantsar da shi ba.

- Ahmadu Haruna Dan Zago

Su wanene ke cewa za a rantsar da Gawuna?
Duk wanda ya fadi haka dayan biyu ne ko dai hankalinsa ba cikakke ba ne ko kuma ba shi da ilmin zamani da na addini da sanin rayuwa.

A cewar ‘dan siyasar, na ukun da zai ce Nasiru Gawuna zai gaji Abdullahi Ganduje shi ne wanda bai san abin da ake kira da damukaradiyya ba.

Hira da Layan NNPP

Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci ya yi karin haske a kan shari’ar zaben Kano, an ji labari ya yi kaca-kaca da masu wannan tunani.

Lauyan ya fada mana tun farko Jam’iyyar APC tayi kuskure wajen shigar da kara a kotun zabe, ya ce tamkar Abba Yusuf ya dare kan mulki ne.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN