Wata sabuwa: Atiku Ya Karfafawa Yan PDP Gwiwa, Ya Ce Har Yanzu Bai Cire Ran Zai Zama Shugaban Kasa Ba


Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya kara jaddada cewa har yanzu shi kam bai yadda ya fadi zaben da aka gudanar na shugaban kasa ba. Legit Hausa ya wallafa.

Atiku ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya halarci liyafar da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ta gayyace shi don tarban sabbin zababbun gwamnonin jam’iyyar da taya murna ga gwamnonin da suka samu komawa karo na biyu a Abuja a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu.

Dan takarar shugaban kasan ya ce dole su tsaya tsayin daka su kuma hada karfi da karfe don ganin sun kwato wannan mulki da aka wafce a hannunsu ba bisa ka’ida ba, cewar jaridar Tribune.

Ya shawarci ‘yan jam’iyyar da su nutsu su duba yadda jam’iyyar ta samu koma baya, bayan ta kasance jam’iyyar da tafi dadewa da kuma karfi tun shekarar 1999, da kuma halin da yanzu take ciki

Atiku ya ce:

“Nan gaba irin wannan biki ya kamata ku sanar mana da wuri saboda mu samu lokacin da zamu tattauna matsalolin jam’iyyarmu da yadda za a shawo kansu.
“Zan yi amfani da wannan dama in taya ku murnan samun nasara, da kuma wadanda suka samu dawowa karo na biyu a ofisoshi daban-daban.”

“Muna da matsaloli daban-daban a wannan jam’iyyar, a baya munfi kowace jam’iyya karfi tun shekarar 1999 amma tun a lokacin muke koma wa baya, lokaci ya yi da ya kamata mu binciki matsalolinmu don mu dawo da martabarmu ta baya.

“Mun sani PDP ba ta fadi zaben da aka yi ba, mu tsaya mu natsu mu kwato mulkin da aka sace daga gare mu.”

A jawabinsa, jaridar Punch ta ruwaito tsohon mataimakin Najeriya, Namadi Sambo ya na kira ga ‘yan jam’iyyar da su zauna lafiya, inda ya koka kan yadda rikicin jam’iyya ya yi kamari a matakin jihohi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN