Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana yaƙinin cewa Najeriya zata ci gaba da bunƙasa karkashin shugabancin zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. Legit ya wallafa.
Buhari ya yi wannan furuci ne a wurin bikin karrama Tinubu da lambar girmamawa mafi daraja GCFR a taƙaice da kuma karrama Kashim Shettima a Abuja.
Channels tv ta ce a wurin taron wanda ya gudana a ɗakin taro na fadar shugaban kasa ranar Alhamis, Buhari ya faɗawa Tinubu cewa:
"Mutanen Najeriya sun gano kwarewarka a shugabanci, gogewar siyasa da kuma burin bautawa ƙasar nan shiyasa suka zaɓe ka suka ɗora maka nauyin shugabancin ƙasar da suke ƙauna."
Banda tantama Najeriya zata ƙara bunkasa kuma ta cimma matsayi mai girma a karkashin mulkinka. Ka fi kowa cancanta a cikin yan takarar da suka shiga zaɓe kuma 'yan Najeriya suka zakulo ka."
Shugaba mai barin gado ya ce tarihin abinda Bola Tinubu ya yi a matsayin gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007 ya isa ya nuna sadaukarwan zababben shugaban ƙasa domin jin daɗin al'umma.
A cewarsa, shugaba mai jiran gado mutum ne mai ƙaunar haɗin kan ƙasa kuma ya bayyana haka ƙarara a tarihin siyasarsa na baya.
Ƙasar nan na cikin kalubale - Buhari
Bugu da ƙari, Buhari ya ƙara tunawa Tinubu da Shettima cewa ƙasar nan tana fuskantar kalubale masu yawa, don haka akwai bukatar su zage dantse da zaran sun karbi mulki ranar Litinin mai zuwa.
Ranar 29 ga watan Mayu, 2023, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai koma gefe ya miƙa wa Bola Tinubu ragamar mulki.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI