Gana ya rasu ne a ranar Alhamis, 25 ga Mayu, 2023, a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Nguru bayan gajeriyar rashin lafiya.
Yana daga cikin shugabannin kwamitin riko na kananan hukumomi 17 da gwamna Mai Mala Buni ya rantsar a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu.
Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamnan Jihar Yobe, Mamman Muhammad, ya tabbatar da rasuwar Karasuwa a wajen taron wayar da kan jama’a da Kwamishinan Ma’aikatar Samar da Arziki da Aikin yi ta Jihar ta shirya.
Gana ya rike mukamin shugaban karamar hukumar Karasuwa na tsawon watanni shida kafin Gwamna Mai Mala Buni ya rusa kwamitin.
Daga nan aka sake nada shi a matsayin shugaban riko na karamar hukumar Karasuwa LG.
A tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007, an zabi marigayin a matsayin dan majalisar dokokin jihar Yobe mai wakiltar Karasuwa a karkashin jam'iyyar PDP.
Ya kuma kasance dan takarar gwamna a PDP a 2015 amma ya koma APC a 2019.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI