Yadda wata Kotu ta gafarta wa barawon dankali a jihar arewa, duba dalili


A ranar Alhamis ne wata kotu da ke zamanta a yankin Kabusa, Abuja, ta saki wani matashi dan shekara 26 mai suna Sulatiyo John da ake tuhuma da laifin satar manyan dankali guda biyar a cikin coci.

 Ana tuhumar John da ke zaune a Durumi l, Abuja da laifin sata. PM News ya rahoto.

 Ya amsa laifin da ake tuhumar sa da cewa yana jin yunwa lokacin da ya saci dankalin.

 Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Malam Abubakar Sadiq ya ce: “Da ganin dan karamin dankalin da aka sata, kotu za ta yi muka sassauci.

 “An sake ka, kuma an gargaɗe ka kada ka sake yin irin wannan aikin.

 “Na gaba idan aka sake gabatar da kai kam irin wannan laifin a gaban kotu, za a dauki mataki mai tsanani a kan ka.

 "An kuma yi muka gargaɗin kada ka sake ziyartar harabar cocin."

 Tun da farko, Lauyan masu gabatar da kara, Mista O.S.  Osho ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 288 na kundin laifuffuka.

 Osho ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya sace manyan dankalin ne guda biyar a harabar cocin.

 Ya bayyana cewa yayin binciken ‘yan sanda, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata satar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN