Mutumin Da Ya Taka Daga Gombe Zuwa Abuja Domin Buhari Ya Ce Zai Maimaita Idan Ya Samu Dama, Ya Ce Bai Yi Nadama Ba


Dahiru Buba, ɗan shekara 53, ya ce ko kaɗan be yi danasanin tattakin da ya kwashe kwanaki 15 ya na yi daga Gombe zuwa Abuja ba domin taya Buhari murnar lashe zaɓe a 2015. Legit ya wallafa.

Buba ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN ranar talata a garin Gombe, inda ya bayyana cewa Buhari ya cikawa 'yan Najeriya gurikansu a shekaru takwas da ya yi yana mulki.

Buhari ya yi iya bakin kokarinsa

Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na gari, wanda ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen yin ayyukan da suka dace saboda soyayyarsa ga ƙasar tasa.

Ya ƙara da cewar gwamnatin Buhari ta yi ƙoƙari sosai, musamman ma wajen yaƙar 'yan ta'addan Boko Haram, waɗanda suka kusa amshe ƙaramar hukumarsa ta Dukku da ke jihar ta Gombe.

Ɗahiru ya ƙara da cewar irin zaman lafiyar da al'ummar yankunan da matsalar Boko Haram ta shafa a baya suke samu a yanzu, ba za ta iya misaltuwa ba kamar yadda Vanguard ta yi rahoto.

Ban yi tattaki a banza ba

Ya kuma bayyana cewa, idan ya tuno da batun tattakin kwana 15 da ya yi daga Abuja zuwa Gombe a shekarar 2015, ya na ji a ransa cewa bai yi tattakin a banza ba.

Ya ce:

“Ko a yanzu in da ace zan samu dama, to zan iya maimaita tattakin saboda shugaban Æ™asar.”

Dangane da masu sukar gwamnatin ta Buhari, Buba ya ce ai dama ba dole ba ne shugaban ƙasar ya iya yi wa kowane ɗan Najeriya duk abinda ya ke so.

Ya ƙara da cewa duk wanda ya ke ganin Buhari ya saɓa masa, to ya yi haƙuri ya yafe masa.

Daga ƙarshe, Dahiru ya taya gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya murnar nasarar lashe zaɓen gwamna da ya ƙara yi a zaɓen da ya gabata.

Ya kuma godewa gwaman, saboda kyautar mota da kuma kuÉ—aÉ—e da ya yi masa a shekarar 2020 saboda tattakin da ya yi wa Buhari.

A shekarar 2020, Channels TV ta yi rahoto kan kyautar motar da gwamnan jihar ta Gombe Inuwa Yahaya ya bawa Dahiru Buba, da kuma wasu kuÉ—aÉ—e a dalilin wannan tattaki da ya yi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN