Type Here to Get Search Results !

Inna lillahi: Yan mata 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a jihar Sakkwato


’Yan mata 15 sun yi arba da ajali a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a kauyen Dandeji da ke Karamar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

Lamarin wanda ya auku a safiyar wannan Talatar bayanai sun ce kwale-kwalen ya kife da ’yan matan da ke kan hanyarsu ce ta zuwa diban itace. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito daga wani ganau da lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce mahaya kwale-kwalen wadanda dukkansu ’yan mata ne aun haura mutum 40 a lokacin da lamarin ya faru.

Wani mazauni yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce gwanayen ninkaya sun tsamo gawarwakin mutum 15 yayin da ake ci gaba nutso wajen lalubo sauran da lamarin ya rutsa da su.

Shugaban Karamar Hukumar Shagari, Aliyu Abubakar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an soma shirye-shiryen gudanar da jana’izar mamatan da mai yanke kauna ta yi wa halinta.

Ana iya tuna cewa, a shekarar biyun da suka gabata, hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 33 wadanda mafi akasari mata ne da kananan yara a kauyukan Ginga da Gidan Magana a jihar ta Sakkwato.

Kazalika, wasu mabiya darikar Tijjaniya sun riga mu gidan gaskiya a irin wannan yanayi yayin bukukuwan Maulidi a bana

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN