Tashin hankali yayin da WHO ta ce annobar da ta fi COVID-19 na nan tafe


Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta gargadi mutanen duniya da su shirya wa wata annoba da ta fi cutar COVID-19 muni nan ba da jimawa ba.

Shugaban hukumar, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ne ya bayyana hakan ranar Talata, yayin taron lafiya na duniya karo na 76 da yake gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland. Jaridar Aminiya ta rahoto.

A cewarsa, “Akwai barazanar wata sabuwar nau’in cuta mai saurin yaduwa kuma mai saurin kisa, kuma har yanzu akwai barazanar cewa wannan cutar na iya bulla.

“Ba wai annobar cututtuka kawai muke fuskanta ba a duniyarmu yanzu haka. Shi kansa tsarin lafiya na duniya cikin tsananin bukata, kuma ya zama wajibi a tashi tsaye domin magance kalubalansa,” in ji shi.

Gargadin na zuwa ne ’yan makonni bayan Shugaban na WHO da kansa ya bayyana kawo karshen cutar ta COVID-19 a matsayin wata annobar ta duniya.

Sai dai ya ce babban taron na bana a kan lafiya wata babbar dama ce ga shugabanni a kowanne mataki su fito da nagartattun hanyoyi wajen magance su.

Bai dai bayyana sunan cutar ba, amma ya bukaci kowa da kowa da ya yi kyakkyawan shiri wajen yin maganinta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN