Girma ya fadi: Sojoji Sun Cafke Wani Basarake Mai Hada Baki Da 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya


Sojoji sun kai sumame a ƙauyen Janjala cikin ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, inda suka cafke Madakin Janjala, Mallam Ibrahim Aliyu, da wasu mutum 13 masu ba ƴan bindiga bayanai. Legit ya wallafa.

Wani majiya wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya gayawa jaridar Daily Trust cewa, sojojin sun shigo garin ne ranar Talata akan motoci 8 ƙirar Hilux, da babura sannan suka tafi da waɗanda ake zargin.

Ya ce sojojin sai da suka tsaya a Kagarko inda nan suka cafke wasu da ake zargi, kafin su ƙaraso zuwa ƙauyen Janjala, wanda ke da nisan kilomita 3 daga Kagarko.

"Mutum biyun da ake zargi da aka kama a Kagarko sun yi wa sojojin jagora zuwa wasu gidaje a Janjala, inda suka ƙara cafke wasu mutum 11." A cewarsa.

Wani mazaunin Janjala mai suna, Yahuza Suleiman, ya bayyana cewa sojojin sun tafi da Madakin garin zuwa Kaduna, saboda sace-sacen mutane da ake yi a ƙauyen.

"Sannan tun sanda sojoji suka tafi da Madaki da wasu waɗanda ake zargi, lambar wayar sa ba ta tafiya, amma wani wanda na samu na yi magana da shi yau da safe, ya gaya min cewa yana can yana amsa tambayoyi a Kaduna, kan sace-sacen mutanen da ake yi a Janjala." A cewarsa.

Ƴan bindiga dai sun daɗe suna addabar ƙauyen Janjala da ƙauyukan da ke makwabtaka da shi, inda suke sace mutane da halaka wasu daga cikin su

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN