Da dumi-dumi: Saurayi ya yi ajali mahaifiyarsa bayan ya dinga caka mata wuka har ta mutu a jihar arewa


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano a halin yanzu suna neman wani matashi mai suna Ibrahim Musa mai shekaru 22, wanda ake zargin ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira.

 Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6: na yammacin ranar Laraba, 3 ga watan Mayu, a unguwar Rimin Kebbe Quarters, karamar hukumar Nassarawa ta jihar.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa Haruna, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce marigayiyar, Hajara Muhammad, an daba mata wuka mai kaifi.

 Hukumar ta PPRO ta ce a halin yanzu Yan sanda sun dukufa don tabbatar da kama wanda ake zargi da ya gudu.

 “A ranar 3 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 1800 na yamma, an samu rahoton cewa wani Ibrahim Musa, ‘m’ mai shekaru 22 a unguwar Rimin Kebbe Quarters, karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano, ya daba wa mahaifiyarsa Mai shekara 50, wata Hajara Mohammed, ‘f’ wuka a sassa daban-daban na jikinta Kuma ya gudu daga wurin," in ji PPRO.

 “An dauji gawar da ke da raunuka da dama daga wurin cikin jini, sannan aka garzaya da ita asibitin kwararru na Mohammed Abdullahi Wase Kano inda wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwar gawar.

 “An gano wata wuka mai tabon jini da ake zargin anyi amfani da ita wajen kai harin a wurin.  A halin yanzu sassan kwararrun Yan sanda sun dukufa aiki don tabbatar da kama mai laifin.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN