Da Ɗumi-Ɗumi: Fitaccen Sarkin Da Aka Tsige Daga Kan Karagar Sarauta a Najeriya Ya Mutu


Sarkin masarautar Okeigbo da ke ƙaramar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo a jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya, Oba Lawrence Oluwole Babajide, ya riga mu gidan gaskiya. Legit ya wallafa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Sarkin, wanda sunan sarautarsa, Oluoke na Okeigbo, kuma aka masa laƙabi da 'Bamigbala na I' ya mutu yana ɗan shekara 92.

Kotu ta tsige Marigayin tun yana da rai

Legit.ng Hausa ta gano cewa a watan da ya gabata, babbar kotun jihar Ondo ta tsige marigayi Oba Babajide daga kan karagar mulki.

Kotu ta ɗauki wannan mataki ne kasancewaɗ Basaraken bai fito daga gidan Sarautar Aare Kugbaigbe na Okeigbo ba, kuma gidan ne ke da alhakin samar da sabon Sarki a shekarar 2018.

Sai dai Oba Babajide bai gamsu da hukuncin da Kotun ta yanke ba, sakamakom haka ya ɗaukaka kara gabanin rai ya yi halinsa.

Yasuhe Sarkin ya kwanta dama?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baba Loja na masarautar Okeigbo, Chief Akinbobola Adedigbo, ne ya sanar da rasuwar basaraken a babban kasuwar garin da safiyar Jumu'a 5 ga watan Mayu, 2023.

Haka zalika a wata sanarwa da mai magana da yawun fadar sarkin, Yarima Alexander Omojadegbe, ya fitar, ya ce tuni waɗanda ke da alhaki suka fara shirye-shiryen jana'iza.

Ya ce tuni mahukuntan fada suka fara duk wani shiri da ya dace na binne mamacin domin ya tafi cikin salama.

Marigayi Oba Babajide ya kasance Oluoke na Okeigbo na 6 a tarihin kafuwar Masarautar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN