Karbar mulki a Kebbi, Gwamna Nasir Idris ya yi jawabi da ya dau hankalin jama'a

Karbar mulki a Kebbi, Gwamna Nasir Idris ya yi jawabi da ya dau hankalin jama'a 



An rantsar da Dr Nasir Idris a matsayin Gwamnan jihar Kebbi bayan ya karbi ragamar mulki daga tsohon Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu.

Da safiyar ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Nasir Idris ya karbi mulki tare da rantsuwar kama aiki a filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi.

Ya bukaci al'ummar jihar Kebbi su zo a hada hannu don ciyar da jihar Kebbi gaba.

Nasir Idris ya ce Gwamnatinsa za ta zakulo hazikan mutane a fadin jihar domin a tafiyar da Gwamnati don ciyar da jihar Kebbi gaba.



Ya kuma ce zai kwatanta adalci wajen tafiyar da gwamnatinsa. Haka zalika ya ce zai mayar da garin Birnin kebbi zuwa birni da kowa zai yi alfahari da shi a matsayinsa na dan jihar Kebbi.

Ya ce zai kuma gyara manyan garuruwan masarautun jihar nan don basu fasali na zamani abin alfahari ga yan jihar Kebbi.

Kazalika ya tabo bangaren tsaro, ilimi, noma da kasuwanci wanda ya ce zai inganta bangarorin ta hanyar amfani da masana da kwararru don ganin an ci ma nassarar manufar da aka fuskanta.

Mai gabatarwa a wajen taro, Malam Isyaka Easy ya ce lokacin danniya, bangaranci, takura da nuna banbanci ya zo karshe a shugabancin jihar Kebbi. Ya ce lokaci ne na mutunta Sarakunan jihar Kebbi da jama'arsu gaba daya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN