A wani yanayi da za a iya kira da sabon salo, Daniel Bwala, hadimin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya taya sabon shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima murnar kama aiki.
Yan mintoci kadan bayan rantsar da Tinubu da Shettima a matsayin shugabanni, Bwala ya garzaya shafinsa na Twitter don taya sabbin shugabannin na Najeriya murna. Legit ya wallafa.
Hadimin Atiku ya taya Tinubu da Shettima murna
Ya roki Allah ya ba sabbin shugabannin hikima da karfin gwiwar shugabantar kasar da kyau.
Ya rubuta a shafin nasa:
"Bari na taya Bola Ahmed Tinubu @officialABAT da Kashim Shetima @KashimSM murnar daukar rantsuwar kama aiki da mubaya'a a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasar Najeriya na 16 don kare kundin tsarin mulki da kuma jan ragamar kasar Najeriya. Ina rokon Allah madaukakin sarki ya baku hikima da karfin shugabantar wannan kasa mai albarka da gaskiya da amana. Ina taya ku murna ba tare da la'akari da siyasa ba."
BY isyaku.com