Type Here to Get Search Results !

Main event

Fusatattun matasa sun kashe barawon babur sun kone gawarsa a jihar ArewaWasu fusatattun mutane sun kashe wani da ake zargin barawon babur ne kuma sun bankawa gawarsa wuta a kusa da babbar kasuwar garin Gombe.

Ana zargin mutumin ne da sace babur ne da wani kwastoman banki ya ajiye a gaban bankin Ja’iz, ya shiga don karbar kudi, inda fusatattun mutanen suka cinna masa wuta. Jaridar Aminiya ta rahoto.

Wani da lamarin ya faru akan idonsa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce barawon ya nemi ya tsere da babur din.

Sai dai a lokacin da mai babur din ya fito ya yi ihun barawo inda nan take ’yan acaba suka bi shi aka kama shi.

Ya ce jama’a cikin fushi suka dinga dukansa suna buga masa dutse kafin daga bisani suka kashe shi suka cinna wa gawar wuta.

Ya Kara da cewa bayan an Kona Barawon jami’an Yan sanda sun zo wajen sun tattara gawar suka tafi da ita.

“Sai mai babur din da ya yi sauri ya bar wajen domin yana tsoron tambayoyin da zai fuskanta daga jami’an ’yan sanda a lokacin bincikensu,” in ji shi.

Da yake tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, cewa ya yi tuni wanda ake zargin aka tafi da gangar jikinsa zuwa asibiti don tabbatar da mutuwar sa ko akasin haka.

Ya ce jami’an su sun isa wajen da lamarin ya faru cikin gaggawa inda suka tattara gangar jikin zuwa asibiti.

Sai dai duk da kona barawon, Kakakin ’yan sandan ya ce lilkitoci ne kawai za su iya tabbatar da mutuwarsa.

Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, inda ya ce hakan ba daidai ba ne.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies