Gwamnoni 5 Masu Barin Gado Wadanda Ba Za Su Mika Mulki Yadda Ya Kamata Ba Da Kuma Dalilin Hakan


Gabanin ranar 29 ga watan Mayu da wa'adinsu zai ƙare a hukumance, ana sa ran miƙa mulki ga waɗanda za su gaje su kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Sai dai saboda wasu dalilai, wasu daga cikin gwamnoni masu barin gado, ba dole ne su yi abin da ya kamata ba wajen miƙa mulkin. Legit Hausa ya wallafa.

Domin kuwa ana zargin waɗannan gwamnoni da ƙin bai wa kwamitocin amsar mulki na zaɓaɓɓun gwamnonin jiharsu haɗin kai.

Takun-saka tsakanin kwamitocin miƙa mulkin da gwamnoni masu barin gado, ya samo asali ne daga tambayoyi kan halin da kuɗin jihohin ke ciki da kwamitocin ke yi.

Ga dai jerin sunayen gwamnonin biyar masu barin gado da suka shiga cikin wannan rukuni:

Bello Matawalle

Ana zargin gwamnan jihar Zamfara da ƙin bayar da haɗin kai ga kwamitin da Dauda Lawal Dare ya kafa, gabanin ƙaddamar da gwamnatin PDP a jihar a ranar 29 ga watan Mayu.

Rahotanni sun bayyana cewa, Dauda Dare ya kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka kashe kuÉ—aÉ—en ma’aikatun jihar, hukumomin bada tallafi masu zaman kansu (MDAs), matakin da gwamnatin jihar ta yi watsi da shi.

Samuel Ortom

Gwamnan jihar Benuwai ma dai ba ya ga-maciji da zaɓaɓɓen gwamna Rabaran Hyacinth Alia na jam'iyyar APC. Kwamitocin miƙa mulki da bangarorin biyu suka kafa sun kasance cikin cece-kuce.

Kwanannan aka jiyo Ortom ya yi alƙawarin miƙa wa Alia a ranar 28 ga Mayu, kwana guda gabanin ranar da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada don miƙa mulki.

Abdullahi Ganduje

Kwamitin miÆ™a mulki da sabuwar jam’iyya mai kayan marmari (NNPP) ta kafa a Kano, ya zargi gwamna mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje da rashin bayar da haÉ—in kai.

Kwamitin wanda ke ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Bappa Bichi, ya bayyana cewa sai bayan wani taron manema labarai ne suka fara samun haɗin kan gwamnan, amma duk da haka ba kamar yadda ake tsammani ba.

Okezie Ikpeazu

Ana zargin gwamnan jihar Abia mai barin gado shi ma da ƙin bayar da haɗin kai ga kwamitin da zaɓaɓɓen gwamnan, Alex Otti ya kafa.

Mambobin kwamitin na Otti sun yi ƙorafin cewa ayyukansu ka iya samun tasgaro, saboda jinkirin fitar da takardar miƙa mulki.

Simon Lalong

Shugaban kwamitin miƙa mulki na jihar Filato, ya ce shirin miƙa mulki na nan lafiya lau, amma ƙaramin shugaban kwamitin ya bayyana akasin haka, in ji rahoton The Punch.

Yiljap Abraham, shugaban kwamitin watsa labarai ya yi zargin cewa gwamnatin Lalong mai barin gado ba ta fitar da kuɗaɗe isassu ba don shirye-shiryen bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN