Yanzu yanzu: Gwamna Bagudu ya amince da biyan kusan N4b kudin gratuti na tsoffin ma'aikatan jihar


Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da biyan kudin gratuti na tsoffan ma'aikatan jihar da suka yi ritaya tun daga 2017.

Shugaban ma'aikatan jihar Kebbi Alhaji Sufiyanu Garba Bena ya sanar da haka ga manema labarai ranar Alhamis a ofishinsa da ke garin Birnin kebbi.

Bena ya ce Gwamnan jihar Kebbi ya amince da biyan Naira biliyan uku, miliyan dari tara da miliyan goma sha daya kudaden gratuti na tsoffin ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi tun 2017/2018/2019 har da wadanda aka tantance daga 1 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Mayu 2023.

Ya ce kudaden sun shafin rukunin ma'aikatan LGEA , L.Govt da kuma state government. Ya kuma ce an sami sarkakiya na a baya kan lamarin, kuma yanzu an kammala tantancewa, sakamakon haka Gwamna ya amince da biyan kudaden.

Bena ya ce adadin ma'aikatan da aka tantance kuma aka biya sun kai adadin 820. Wanda suka hada da 355 a matakin Gwamnatin jiha, 250 na L.govt da kuma 210 na LGEA.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN