Daga karshe ta bulla: Ainihin dalilin ganawar Tinubu da Kwankwaso da Sanusi II a Faransa


Bayanai sun kara fitowa game da ganawar sirri da shugaban kasar Najeriya mai jiran gado, Bola Tinubu da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso da kuma Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II a birnin Paris na kasar Faransa.

Aminiya ta ruwaito cewa Tinubu ya sa labule da Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, da nufin jawo shi su yi aiki tare bayan rantsar da Gwamnatin Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki. Rahotun Jaridar Aminiya ta wallafa.

Kwankwaso ya tabbatar da gawawar, inda aya ce a ranar Alhamis zai yi karin bayani a kai, kamar yadda kafar yada labarai ta TRT Afrika ta ruwaito shi.

Majiyoyi masu tushe sun shaida wa Aminiya cewa Tinubu ya kuma yi ganawar sirri da Sanusi II, haka shi ma Kwankwaso ya yi wata ganawar da tubabben sarkin.

“Manufar tattaunawa ukun da aka yi su daban-daban ita ce aniyar zababben shugaban kasan na yi aiki da wadannan manyan mutanen daga Jihar Kano,” in ji daya daga cikin majiyoyin.

“Kwankwaso dan siyasa ne mai dimbin magoya baya a Kano da ma fadin Arewacin Najeriya, Sarki Sanuni II kuma kwararre ne a fannin tattalin arziki da kasar nan ta shaida muhimmiyar rawar da ya taka a lokacin da yake Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),” in ji daya majiyar.

Ganawar farko

Majiyoyinmu sun shaida mana cewa a yayin ganawar Tinubu da Kwankwaso na tsawon awa hudu a birnin Paris, shugaban kasa mai jiran gado ya bukaci Kwankwaso ya jawo hankalin abokan siyasarsa kan muhimmancin su zo a tafi tare domin cigaban kasa.

An yi wa Kwankwaso tayi
Sun kuma amince za su ci gaba da tatatunawa, sannan ya yi wa bangaren Kwankwaso tayin wasu kujerun ministoci.

“Ya bukaci jagoran na NNPP ya zabi tsakanin kujerar Ministan Ilimi ko Ministan Noma,”in ji majiyar.

Sai dai babu tabbacin ko Kwankwaso ne zai rike mukamin ne ko kuma zai ba wa mukarrabansa ne a gwamnatin hadakar.

“Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya halarci zaman, wanda Kwankwaso ya samu rakiyar zababben dan Majalisar Dattawa na Kano ta Tsakiya, Abdulmumin Jibrin.

“Matar Tinubu, Sanata Oluremi ce ta karbi bakuncin matar Kwankwaso, Hajiya Hafsa, a yayin da ’yan siyasar suka tattauna a kan hadin kan kasa da abubuwan da sabuwar gwamnati za ta ba wa muhimmanci, wadanda Kwankwaso ya yi na’am da su.

“Sun kuma yi waiwaye a kan kawancensu na siyasa tun suna lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Kasa a shekarar 1992,” in ji majiyar.

Ganduje da Kwankwaso

Ta ce an kuma fara tunanin sulhu tsakanin Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, wato Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2015 Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso, amma ba da jima ba suka raba gari, kuma har yanzu ba sa ga-maciji.

Muhimmancin Kwankwaso ga Tinubu

Ana iya tuna cewa duk da yake Kwankwaso ne ya zo na hudu a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 da Tinubu ya lashe, tsohon gwamnan Kanon ne lashe kuri’un jihar Kum babbar cibiyar jam’iyyar Tinubu ta APC, duk kuwa da cewa Ganduje ne gwamna.

Jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP ta kuma lashe biyu daga kujerun sanata uku na jihar, da 17 daga kujerun majalisar tarayya 24, gami da kujerun 26 cikin kujerun majalisar dokokin jihar guda 40.

Atiku da Obi sun je kotu

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu, da Peter Obi na LP, wanda ya zo na uku, suna kalubalantar nasarar Tinubu a gaban kotu inda kowannensu ke ikirarin lashe zaben amma an murde masa.

Muhimmancin Arewa

Tinubu na ganin cewa duk da cewa Kwankwaso ya kayar da shi a zaben shugaban kasa a  Kano, kuri’un da ya samu a jihar da kuma daukacin yank in Arewa maso Yamma sun taka muhimmiyar rawa wajen kaiwarsa ga nasara; Don haka yake yin duk mai yiwuwa wajen jawo yankin a jika.

Tinubu ya samu kuri’u 2, 652, 235 daga yankin, wanda shi ne kaso 30 cikin 100 na kuri’un da ya samu a fadin kasar.

Alakar siyasa tsakanin Tinubu da Kwankwaso dai ba sabuwa ba ce, hasali ma a tare suka kafa jam’iyyar APC gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2015, kuma jam’iyyar ta kayar da shugaban kasa mai Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa.

Ganawar Tinubu da Sanusi II

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da abin da Tinubu ya tattauna da Sarki Sanusi II na tsawon awa biyu, amma majiyarmu ta ce hakan ba zai rasa nasaba da siyasar Jihar Kano ba.

Aminiya ta ruwaito cewa akwai rade-radin gwamnatin NNPP mai jiran gado a Jihar Kano za ta waiwayi batun tsige Sarki Sanusi II da Gwamnatin Ganduje ta yi a shekarar 2020 bisa zargin rashin ladabi, inda ta maye gurbinsa da tsohon Sarkin Bichi, wato Sarki Aminu Ado Bayero mai ci a yanzu.

A wata hira da aka yi da shi a watan Afrilu bayan kammala zabe, an ji Kwankwaso na cewa Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf zai iya waiwayan batun, da ma na na kafa sabbin masarautu da gwamnatin Ganduje ta yi.

Sai dai a martanin Ganduje yayin taron bikin ranar ma’aikata, ya ce sabbin masarautun da gwamnatisa ta kafa, sai mahadi-ka-ture.

Tattaunawar Kwankwaso da Sanusi II

Babu cikakken bayani game da abin da Kwankwaso suka tattauna da Sanusi II.

Amma majiyarmu da ta tabbatar da an yi zaman, ta ce shugabannin biyu sun jima suna kare juna.

Idan za iya tunawa Kwankwaso ya yi ruwa da tsaki wajen nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano jim kadan bayan Gwamnatin Goodluck Jonathan ta dakatar da shi daga aikinsa na Gwamnan Bankin CBN.

Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya gabanin ranar 29 ga wata da zai karbi rantsuwa a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN