Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan maramari, Rabiu Kwankwaso, ya tabbatar da rahoton cewa ya gana da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
A wata hira da kafar watsa labarai TRT Afrika, tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, ya ce ba zai bayyana abinda suka tattauna ba sai ranar Alhamis mai zuwa. Legit ya wallafa.
Idan baku manta ba, shugaban Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Kwankwaso, jagoran NNPP da kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a ƙasar Faransa ranar Talata.
Ƙarin bayani na nan tafe...
BY isyaku.com