Shugaba Bola Tinubu ya umurci ma’aikatar tsaron DSS a kasar da ta gaggauta ficewa daga ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ke Ikoyi a Legas.
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Tunde Rahman ya sanya wa hannu, ta ce shugaban ya bayar da umarnin ne biyo bayan rahotannin da ke cewa jami’an DSS sun kai farmaki ofishin EFCC da ke kan titin Awolowo, Ikoyi, Legas a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, inda suka hana jami’an hukumar shiga wurin aikinsu.
“Shugaban ya ce idan akwai batutuwan da ke tsakanin manyan hukumomin gwamnati biyu, za a warware su cikin ruwan sanyi.” Inji sanarwar.
BY isyaku.com