Yan bindiga sun kashe Yan sandan kwantar da tarzoma 6 da mutane 30 a kauyukan Masarautar Zuru jihar Kebbi


Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sandan kwantar da tarzoma Mopol 6 da wasu mutane 30 a kauyen Dan Umaru da ke karamar hukumar Danok Wasagu a yankin Masarautar Zuru a jihar Kebbi.

 An kai harin ne da sanyin safiyar Lahadi, 30 ga Afrilu, 2023.

 An kuma yi garkuwa da mutane da dama tare da sace daruruwan shanu yayin harin da aka kai kauyukan da ke makwabtaka da su.

 Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, mazauna garin sun ce an yi jana'izar mutane 27 yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.

 Har yanzu dai hukumomin ‘yan sanda a jihar ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

 A halin da ake ciki dai, abokai da 'yan uwa da abokan aiki sun yi ta yada hotunan jami'an 'yan sandan da aka kashe a shafukan sada zumunta. Yayin da suke masu addu'a da jajenta wa iyalansu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN