Da Dumi-Ɗumi: Wani Mummunan lamari ya auku bayan Manyan Malamai Uku Sun Mutu a Wani Hatsarin Mota


Mutum huɗu, waɗanda suka ƙunshi Malaman Addinin Kirista guda 3 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da rutsa da su a jihar Ekiti. Legit ya wallafa.

Leadership ta rahoto cewa hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Litinin a kan Titin Otun–Iro Ekiti, ƙaramar hukumar Moba a jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Baya ga waɗanda suka rasa rayuwarsu, wasu mutum biyar sun ji raunuka kala daban-daban a haɗarin motar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa yan jarida a Ado-Ekiti, babban birnin jihar cewa Mamatan sun taso daga Ipere-Ekiti zuwa Iro-Ekiti lokacin da Ibtila'in ya afka kan motarsu, kuma nan take rai ya yi halinsa."

Sauran waɗanda suka ji raunuka na kwance a Asibitin koyarwa na tarayya da ke Ado Ekiti, suna karɓan magani yayin da gawarwakin waɗanda suka mutu aka aje su a ɗakin ajiyar gawa.

Bayanai sun nuna cewa ɗaya daga cikin Malaman ya samu canjin wurin aiki daga Cocin Ipere Ekiti kuma sauran Malaman biyu sun rako abokinsu zuwa sabon cocin da aka maida shi a Iro-Ekiti sa'ilin da suka gamu da ajalinsu.

An ce sauran Malaman biyu suna wa'azi ne a cocin da kowanensu ke jagoranta a garuruwan Eda Oniyo da kuma Ewu Ekiti.

Wata mata, wacce take da alaƙar yan uwantaka da marigayi Faston da aka sauya wa wurin Wa'azi, tana cikin waɗanda suka mutu a haɗarin.

Yayin da aka tuntube shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Jaridar Punch ta rahoto Abutu yana cewa:

"Mun samu labari kuma mun tura jami'an yan sanda masu kula da harkokin hanya. Sun ɗauki gawar mamatan zuwa Asibiti inda aka tabbatar da rai ya yi halinsa."

"Muna kan nazari kan lamarin kuma bincike ya yi nisa don gano ainihin abinda ya haddasa hatsarin."

Sakamakon rikicin shugabancin da ya ɓarke, dakarun yan sanda sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Abiya.

Wasu yan majalisu sun ware kansu, kuma sun kaɗa kuri'ar tsige kakakin majalisar, hakan ya haddasa rabuwar kai.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN