Abin ban tsoro! Uwa ta kashe danta mai shekara biyar, ta dafa kansa, ta ci naman sassan jikinsa


Wata mata mai shekaru 29 da haihuwa mai suna Hanaa, ta yi wa danta mai shekaru biyar, ta daddatse danta mai suna Youssef da adda a gidansu da ke Masar, kafin ta tafasa ta kuma ci wasu sassan kansa.

 Ana zargin Hanaa ta kashe danta da ba a yi tsammani ba da duka a kai kafin ta yanka gawarsa a bandaki. PM News ta rahoto.

 'Yan sanda sun kama Hanaa bayan da kawun Youssef ya firgita ya gano sassan jikin yaron a cikin bokiti a gidan dangi a kauyen Abu Shalabi.

 Kamar yadda DailyMail ta ruwaito a ranar Talata, matar, wacce ta amsa cewa ba ta da hankali, ta shaida wa ’yan sanda cewa ta ci wani bangare na kan danta ne saboda ta so ya zauna tare da ita, ta kara da cewa ta dafa kan sannan ta dafa kan da sauran sassan namansa a kan murhu a cikin ruwan zafi kafin ta ci.

 Ta ce ba ta da niyyar kashe shi.
 
 Tun lokacin da ta rabu da mijinta, ita da ɗanta suna zaune su kaɗai, kuma ta dage cewa ta san abin da take yi.

 Tsohon mijin wanda aka bayyana sunansa H.A ya ce, “A lokacin da na zo ‘yan sanda sun hana ni ganin dana saboda munin lamarin.

 “Mun rabu da juna shekaru hudu da suka wuce saboda ta dawo daga gidan mahaifinta kuma ta ce in bar gidan da iyalina in tafi da ita mu zauna a fili.

 “Amma na ki, kuma dangantakar ta ƙare gaba ɗaya bisa ga ra'aiynta, kuma na yi ƙoƙari na sasanta da ita bayan rabuwar aure, amma ta ƙi, kuma ta dage kan ra’ayinta.

 Ya ƙara da cewa: ‘Ɗana shi ne kawai dalili da na hada wani abu da ita, kuma nakan gan shi a kai a kai ina kawo masa tufafi da abubuwan da yake bukata.

 ‘Amma kwanan nan tana ƙoƙarin nisantar da shi daga gare ni, ta dasa ƙiyayya gare ni a cikin zuciyarsa, don kada ya zo gare ni.

 Sai dai mahaifiyar yaron ta ce 

‘Na so in rama wa mahaifinsa, in sami ‘yanci.  Mahaifinsa yana ta zuwa yana ƙoƙari ya tafi da shi kullum.'

 Ofishin mai gabatar da kara ya bayyana cewa an tsare wanda ake zargin kuma za a yi mata gwajin tabin hankali.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN