Jam’iyyar APC ta reshen jihar Gombe ta dauki matakin korar wani Sanata mai-ci a majalisar dattawa, bisa zargin ya kitsa mata zagon kasa.
Bayan Sanatan da aka kora, Daily Trust ta rahoto cewa APC mai mulki ta karbe rajistar wani ‘dan majalisa da yake kan kujera saboda wannan zargi.
Wanda aka kora ba kowa ba ne illa Sanata Bulus K. Amos wanda a zaben 2023 bai samu tikitin wakiltar Kudancin Gombe a majalisar dattawa a APC ba.
Shi ma Honarabul Yunusa Ahmad Abubakar mai wakiltar Yamaltu/Deba a majalisar wakilan tarayya bai sha ba, yana cikin wadanda aka hukunta a jiya
Kafin nan, a Afrilu Shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Bambam suka dakatar da jagororin.
Zargin da yake kan su shi ne sun yi wa APC makarkashiya a zaben da ya gabata, su ka mara baya a boye ga ‘yan takaran da suka tsaya a jam’iyyun adawa.
Rahoton bai yi cikakken bayanin laifuffukan wadannan ‘yan siyasa ba. Amma har kullum, cin amanar jam’iyya yana cikin zunubai mafi muni a siyasa
Shugaban APC na Bambam, Muhammad Kaka, ya ce dole su ka kori Sanatan bayan ya gagara bayyana a gabansu domin ya wanke kan shi daga zargi.
Da yake magana a Balanga, Vanguard ta ce Kaka ya nuna Amos ya yaki jam’iyyar APC a zabe.
Musa Awak da Ali Kachalla sun tabbatar da wannan zargi, su ka ce a dalilin Sanatan kudancin jihar ne 'yan takaran APC da-dama suka sha kunyata.
Wani hadimin mataimakin shugaban kwamitin na Neja-Delta a majalisa, Felix Manasseh, ya musanya zargin, yana mai cewa sharrin siyasa ce.
Hakan ya na zuwa ne makonni biyu da APC ta kori Sanata Muhammad Danjuma Goje a kan irin wannan zargi na cin amanar jam’iyyarsa da yake kai.
Mun fahimci ana zargin Sanatan Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje ya goyi bayan jam’iyyar NNPP ne a zaben Gwamna da aka yi a 2023.
BY ISYAKU.COM