Wata mai yin kwalliya mai suna @Queenyetty1 wacce ta bayar da labarin a Twitter, ta tabbatar da cewa lamarin ya auku da gaske. Legit ya wallafa.
A cewarta, matar auren da babbar ƙawarta sun kalli wani bidiyo ne wanda ya nuna girman kayan aikin mazaje.
Sai abin ya birge budurwar, inda tace abinda aka nuna a cikin bidiyon ba gaske ba ne.
Matar auren sai ta bayyana cewa ta yarda ƙarya ne, amma akwai maza masu irin wannan, kuma mijinta yana ɗaya daga cikin su.
Wata shida bayan aukuwar hakan, kawai sai budurwar ta samu juna biyu tare da mijin ƙawarta, sannan ta sha alwashin ƙin zubar da cikin ko rabuwa da mijin ƙawarta.
"Yanzu ƙawarta mai juna biyun ba ta son zubar da cikin ko rabuwa da mijin. Tace ba haka ta so ya faru ba, ta so ne kawai ta ɗanɗana shi kawai a wuce wajen." A cewar mai yin ƙwalliyar.
BY ISYAKU.COM