Ta faru: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu


An fara tunanin cewa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyara jihar ne ba don kaddamar da ayyukan gwamna Nyesom Wike kaɗai ba, akwai wata a ƙasa.

A wata sanarwa da ƙungiyar 'The Centre for Reform and Public Advocacy (CRPA),' ta ce tana zargin akwai wani kulli da jiga-jigan siyasar biyu suka yi yayin wanan ziyara.

A sanarwan wacce ta shiga hannun Legit.ng Hausa, ƙungiyar ta yi ikirarin cewa babbar ajendar Tinubu ita ce ya nemi taimakon Wike domin ya shiga ya rage karsashin karar da jam'iyyun adawa suka shigar Kotu.

Tsagin adawa, wanda ya kunshi jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, Labour Party da Peter Obi, sun garzaya Kotun zaɓe, sun kalulanci matakin INEC na ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar CRPA, Ifeanyi Okechukwu, ya ce an ɗora gwamna Wike kan wannan aikin ne saboda yadda ya ƙosa ya shiga cikin muƙarraban gwamnatin Tinubu.

Okechukwu ya ce:

"Tunda ta bayyana karara Wike ya ƙosa ya samu muƙami a gwamnatin zababben shugaban ƙasa, hakan ya sa aka ɗora shi kan aikin ruguza ƙarar da jam'iyyarsa da LP suka ƙalubalanci nasarar APC."

"Duk da APC ba ta tabbacin ko zai yi aikin amma ba don komai Wike ya gayyato shugaba mai jiran gado ya kaddamar da ginin Kotu a Ribas ba sai don ya gamsar da shi cewa yana da gogewar aiwatar da duk aikin da aka É—ora masa."

Matar Wike zata taka muhimmiyar rawa
An tattaro cewa mai É—akin Wike kuma mace ta farko a jihar Ribas, Mai shari'a Eberechi Suzzette Wike, zata taka muhimmiyar rawa a wannan aikin.

Okechukwu ya kara da cewa gayyato Tinubu wani shiri ne na samun damar da tawagar zababben shugaban ƙasan ta gana da gwamna Wike da nufin cimma matsaya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN