Majalisar dokokin jihar Sokoto a ranar Talata ta zartas da wani kudiri na daidaita kudaden aure a jihar. NAN ya ruwaito.
Kudurin dokar wanda Alhaji Abubakar Shehu (APC-Yabo) da Faruk Balle (PDP- Gudu) suka dauki nauyinsa, an mika shi ga kwamitin kula da harkokin addini na majalisar.
Shehu, wanda shi ne Shugaban kwamitin, ya gabatar da rahoton kwamitin a zauren taron, wanda aka amince da shi gaba daya ya zama doka.
Kudirin ya nemi a kula da yadda ake kashe makudan kudade a auratayya, suna, kaciya da sauran bukukuwan gida a fadin jihar.
Shehu ya ce yayin da yake gabatar da rahoton, kwamitin ya gana da masu ruwa da tsaki wadanda suka bayar da gudunmawa mai kyau, wadanda aka saka a cikin kudirin dokar.
Bayan tattaunawa a zaman da mataimakin shugaban majalisar, Alhaji Abubakar Magaji ya jagoranta, ‘yan majalisar sun amince da kudurin gaba daya nan take da gagarumin rinjaye. .
BY ISYAKU.COM