‘
Yan bindiga sun sako uku daga cikin Yan Mata dalibai bakwai da suka rage na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi da aka sace kimanin shekaru biyu da suka wuce. LIB ya rahoto.
Yan bindiga sun sako uku daga cikin Yan Mata dalibai bakwai da suka rage na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi da aka sace kimanin shekaru biyu da suka wuce. LIB ya rahoto.
Wadanda aka saki sune Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunday da Aliya Abubakar.
Shugaban iyayen kungiyar ‘yan matan makarantar da aka sace, Malam Salim Kaoje, ya bayyana cewa sabbin ‘yan matan da aka sako sun isa birnin Kebbi ne da yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Mayu, 2023.
“Eh sun sako mana uku daga cikin ‘yan matan makarantar ranar Lahadi da yamma. Tuni dai suna tare da gwamnatin jihar,” in ji Kaoje.
Sai dai bai bayyana ko an biya wani kudin fansa ba.
Ku tuna cewa an sace 96 daga cikin daliban FGC lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari makarantar a ranar 17 ga Yuni, 2021.
Yayin da wasu daga cikin wadanda aka sace suka samu ‘yanci jim kadan bayan kai harin, 11 daga cikin daliban sun kasance a hannun ‘yan bindigar.
Idan dai ba a manta ba, an sako hudu daga cikin ‘yan matan, Bilha Musa, Fa’iza Ahmed, Rahma Abdullahi da Hafsa Murtala daga hannun shugaban ‘yan fashin nan, Dogo Gide a watan jiya.
Kaoje ya ce sun biya wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba don ganin an sako ‘yan matan hudu bayan sun sayar da kadarorinsu da kuma wani asusu da ya sa ‘yan Najeriya da dama ke taimaka wa iyayen da kudi.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI