An Kuma Dai: 'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Jami'in Ɗan Sanda Ta Wani Yanayi Mai Ban Tausayi


Miyagun 'yan bindiga sun kashe mataimakin Sufuritandan yan sanda (ASP) wanda ke aiki a hukumar 'yan sanda ta jihar Abiya, daga bisani suka fille masa kai.

The Nation ta tattaro cewa marigayi ASP wanda aka gano sunansa “Agbalagba” a takaice, yana aiki ne a Caji Ofis din Ndiegoro da ke ƙaramar hukumar Aba ta kudu a jihar Abia. Legit ta wallafa.

Rahoton da jaridar ta tattara ya nuna cewa yan bindigan, bayan sheke ɗan sandan da kuma raba kansa da gangar jikinsa, sun yi awon gaba da bindigarsa ta aiki da Kakin 'yan sanda.

Marigayi ASP, ɗan asalin jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya, wanda ke jagorantar tawagar sintiri, yana dab da yin ritaya daga aiki a watan Satumba mai zuwa.


An ce marigayi Agbalagba da yan tawagarsa sun fita aikin binciken ababen hawa da sanyin safiyar Talata a Titin Kamaru daga kuiɓin gabas, ba zato ba tsammanin yan bindigan suka far musu.

Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna, bai ɗaga kiran waya ko amsa sakkonnin da aka tura masa ta ba.

Amma wata majiya a rundunar yan sanda ta tabbatar kisan mataimakin Sufuritandan, inda ta ƙara da cewa tuni aka fara bincike don zakulo duk masu hannu.

Jihar Abiya na cikin jihohin da suke fama da hare-haren yan bindiga waɗanda ake zargin mayaƙan kungiyar ta'addanci IPOB ne, kamar yadda Punch ta rahoto.

Ƙasar Rasha ta zargi Ukraine da yunkurin kai hari fadar shugaban ƙasa Putin ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa guda biyu.

Gwamnatin Ukraine ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa ta maida martani kan wannan zargi da aka rataya mata.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN