Zancen Tinubu: APC ta bukaci kotu da ta yi watsi da karar da jam’iyyu 3 suka shigar


Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta roki kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) da ta yi watsi da karar da Action Alliance (AA), Allied Peoples Movement (APM) da Action People’s Party (APP) suka shigar na neman kada a bayyana Bola Tinubu a matsayin  wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

 Jam’iyyun uku a cikin kokensu na daban, sun kalubalanci ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa. Rahotun PM News.

 A cikin karar, AA, ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), APC, Tinubu da Hamza Al-Mustapha, dan takarar shugaban kasa na bangarenta kuma tsohon CSO ga marigayi Janar Sani Abacha.

 APM, a takardar kokenta, ta bi INEC, APC, Tinubu, Kashim Shettima da Kabir Masari, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa a lokacin zaben fidda gwani kafin a maye gurbinsa da Shettima.

 Sai dai APP ta kai Tinubu, APC da INEC kara kotu a matsayin wandanda aka yi Kara na 1 zuwa 3.

 A cikin kararrakin AA, APM APP da ‘yan takarar su na shugaban kasa suna kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa bisa zargin rashin bin dokokin zabe da kuma ka’idojin INEC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN