Masu garkuwa sun sako tsohon mataimakin Gwamnan jihar Nassarawa bayan karbar kudin fansa N4m


An sako Farfesa Onje Gye-Wado, tsohon mataimakin Gwamnan jihar Nasarawa, wanda aka yi garkuwa da shi a daren ranar Alhamis bayan an biya kudin fansa naira miliyan hudu.

 Daily trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da Farfesan shari’a daga gidansa da ke Rinza kusa da Wamba, hedikwatar karamar hukumar Wamba ta jihar.

 Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 70, amma iyalan sun tattauna daga Naira miliyan 2, daga baya kuma suka biya Naira miliyan 3.5, inda a karshe suka biya Naira miliyan 4 kafin a sako shi.

 Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu cewa, “Masu garkuwa da mutanen sun karbi kudin fansa ne a kusa da makarantar Sakandare ta Mada Hills da ke Akwanga, tare da cajin katin naira 200, bayan sun sako shi daga kogon su da ke kusa da Angwan chiyawa, kusa da tsaunukan da ke tsakanin Akwanga da Nasarawa Eggon.  ”

 An tattaro cewa an mayar da Farfesa Gye-Wado fadar sarkin Wamba, Oriye Rindre, Justice Lawal Musa Nagogo, bayan an sake shi.

 Wani tsohon shugaban kungiyar ta NUJ kuma tsohon kwamishinan yada labarai a jihar, Mista Dogo Shamma, ya tabbatar da sakin Farfesa Gye-Wado, ta hanyar sakon waya.

 "In sha Allahu An sako Farfesa Onje daga hannun masu garkuwa da mutane a yanzu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN