Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin wannan mako, ya yi Allah-wadai da amfani da ta’addanci a matsayin makami wajen rigingimun kabilanci.
Ya kuma bukaci da a nemo wadanda suka aikata kisa kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba a Binuwai, kuma a gaggauta magance yanayin tashin hankali gaba daya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa shugaban na Najeriya ya ba da wannan umarni ne a lokacin da yake yin Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Benue, inda aka kashe gomman mutane a unguwar Umogidi, Entekpa-Adoka a karamar hukumar Otukpo (LGA) a jihar
Shugaban ya bukaci da a yi duk kokarin da za a kawo karshen "mummunan tashin hankali".
Ya kuma umurci jami’an ayyukan sirri, ‘yan sanda da kwamandojin soji da su kara sanya ido a kowane fanni da kuma gaggauta magance rashin tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
BY ISYAKU.COM