Soja ya dirka wa wani mutum harbi a yayin da mutumin ya yi yunkurin kwace akwatin zabe daga hannun jami'an INEC a Karamar Hukumar Fakai ta Jihar Kebbi. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Shaidu sun ce wanda aka harba din tsohon dan haramtacciyar kungiyar tsaro ta sa-kai ne wanda shi da abokansa suka kutsa wata rumfar zabe a matsayin jami'an tsaro.
A nan ne suka yi yunkurin kwace akwatin zabe a hannun jami'an INEC, kuma kokarin mutanen wurin na hana su ya ci tura.
An ce ya yi yunkurin kwace bindiga a hannun wani soja, shi ne sojan ya dirka mishi harbi.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI