An kashe almajiri an kwakule idonsa a Jigawa cikin watan Azumi


Wasu da ba san ko su wane ne ba sun kashe wani almajiri sannan suka kwakule idonsa a Jihar Jigawa.

An tsinci gawar ce bayan an jima ana neman shi, kafin daga bisa aka tsinci gawarsa kwance cikin jini an kwakule masa ido daya. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce kafin a gano gawar, malamin almajirin ya kai rahoto caji ofis cewa tun da yaron ya je neman ice ba a sake jin duriyarsa ba.

Kakakin rundunar, Lawal Shiisu, ya ce malamin mai suna Malam Muhammad Mustafa, “ya yi mana korafi tun da misalin karfe 8 na safiyar Juma’a wani almajirinsa ya tafi nemo ice amma bai dawo gida ba.

“Daga baya aka tsinci gawar almajirin an kwakule masa ido daya,” a kai ta Babban Asibitin Dutse inda likita ya tabbatar ya rasu.

A cewar Shiisu, rundunar ’yan sandan ta fara farautar wadanda suka yi wannan aika-aika.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN