Wata matar da ta zo kada kuri’a a cikon zaben yau Asabar a jihar Kebbi ta bayyana cewa, ‘yan jam’iyyar tsinsiya sun ba ta N3000, atamfa guda biyu da kwalin taliya domin ta zabe su.
Wata matar ta daban, ta ce jam’iyyar ta ba ta irin wadannan kayayyakin domin tabbatar da ta zabe su a zaben da ke gudana. Legit Hausa ya wallafa.
Wadannan matan sun zanta da gidan talabijin na Channels ne a Baban Dutsi Model Primary School da ke da rumfunar zabe uku; Karyo, Umijin Nana da Babban Dutsi.
BY ISYAKU.COM