Kasar Saudiyya ta sanar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal, 1444AH yau Alhamis 29 ga watan Ramadan a wurare kamar Tumair da Sudair. Legit ya wallafa.
A sanarwan da hukumar da ke kula da Masallatai masu Alfarma guda biyu, Haramai Sharifai, ta fitar, ta ce gobe Jumu'a 21 ga watan Afrilu, 2023 ce ranar Eid al-Fitr.
BY ISYAKU.COM