Kutun shariar Musulunci a garin Birnin kebbi ta daure gardi da aka kama ya yin shigar Mata shekara biyu a kurkuku ko biyan tarar N80,000. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.
Wanda ake tuhuma mai suna Nazifi Abubakar ya fuskanci Alkali Gazzali Muhktar ne bayan mai shigar da kara na Yan sanda Shafiu Umar ya gurfanar da shi gaban Kotu ranar Litinin 17 ga watan Aprilu 2023.
Mai gabatar da kara amadadin Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi ya tuhumi Nazifi karkashin sashe na 143 da 151 na dokar Penal Code na jihar Kebbi, bisa tuhumar yin sojan gona don cutarwa, watau Criminal Impersonation da Kuma tayar da hankalin jama'a Public Nuisance.
Mai gabatar da kara ya gaya wa Kotu cewa, Nazifi dan asalin garin Gwandu ne da ke karamar hukumar Gwandu a jihar Kebbi.
Ya ce idan ya bar garin Gwandu ya zo garin Birnin kebbi inda yake zaune a gidan wata Mata sai ya yi shigar Mata.
Mahaifin Nazifi da Yan uwansa wadanda suka zo Kotu, sun shaida wa Kotu cewa basa goyon bayan abin da Nazifi yake yi.
Sai dai Kotu ta tambayi Mai shigar da kara na Yan sanda Shafiu Umar, ko aikwai koke kan Nazifi da ya shafi cin amana na kudi ko dukiya sakamakon yaudara da Nazifi ke yi, sai ya Shafiu ya ce babu.
Bayan ikirarin aikata yin shiga irin na Mata da sauran bayanai da Nazifi ya yi wa Kotu.
Sakamakon haka, Kotu ta kama shi da laifi karkashin sashe na 143 na Penal Code, kuma Alkali Gazzali Muhktar ya yanke wa Nazifi Abubakar hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari ko ya biya tarar Naira dubu tamanin N80,000.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI