An tattaro cewa wadanda lamarin ya shafa, Ibrahim Abubakar Rabah, ma’aikacin POS, kuma wanda ya kammala karatunsa na jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, an sace shi tare da wasu mutane biyu Mustapha Muhammad Rabah da Ummaru Ahmad, sama da wata guda a karamar hukumar Rabah ta jihar.
Abokai da ‘yan uwa da suka tabbatar da faruwar lamarin a Facebook, sun ce ‘yan bindigar sun kashe Ibrahim da Mustapha, bayan sun biya kudin fansa N2m.
BY ISYAKU.COM