Ta faru: 'Yan daba sun kashe dan sanda, sun jikkata wasu jami'ai da yawa a wata jiha


Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sheke ASP na ‘yan sanda tare da jikkata wasi jami’ai a wani farmakin da suka kai kan tirken binciken jami’an da ke Ikorodu a jihar Legas

An kuma ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun tsere da bindigogi biyu na ‘yan sandan da aka ce sun tsaya a magamar Enure da ke Itokin a kusa da babban titin Ikorodu zuwa Abeokuta. Legit ya wallafa.

An tattaro cewa, lamarin ya faru ne a daren Juma’a, kasa awanni 48 kenan bayan da ‘yan bindigan kashe mazauna uku na unguwar Gowon da ke Ipaja kana kasa da awanni 24 da hallaka ‘yan sanda uku a wani yankin jihar Edo.

Majiya ta shaidawa jaridar The Nation cewa, ana zargin wasu matsafa ne suka kai harin, wadanda aka ce sun dauki lokaci suna barna a yankin na Legas.

Hakazalika, an gano cewa, akalla mutane hudu wadannan matsafa suka kashe a yankin Ikorodu, inda aka ce suna aiki ne ga wani mai kwace filayen jama’a.

Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:

“Matsafan na nan a Emuren kuma sun yi kaurin suna. Suna yiwa wani fitaccen mai kwace filayen jama’a aiki ne a Ikorodu.”
A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace ana ci gaba da bincike a kai.

A cewarsa, ba za a bayyana sunaye da bayanan ‘yan sandan da suka mutu ba sai har an sanar da ahalinsu yadda ya dace.

Ya kuma tabbatar da cewa, an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannun a kisan da aka yi a unguwar Gowon a ranar Laraba da dare.

Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis, kuma sun tabbatar da suna da hannu a barnar da ta auku.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN