Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi Allah-wadai da rashin da’a da rashin nuna kwarewar aiki da wasu ‘yan sandan suka yi a cikin faifan bidiyo, inda suka rika harbin bindiga don birgr wani mawaki Dauda Kahutu ‘Rarara’ a jihar Kano kwanan nan.
Bidiyon ya nuna yadda jami’an suka yi wa mawakin rakiya, yayin da suka bude kofar motar SUV da ya shiga, sannan suka rika harbin bindiga a sama suna yi masa rakiya.
A wata sanarwa da ta saki a ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu, kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya yi Allah wadai da ayyukan ‘yan sandan, ya kuma ce an gano su tare da kama su.
“Za a kawo su hedikwatar rundunar domin yi masu tambayoyi da kuma daukar matakin ladabtarwa, irin wannan aikin rashin da'a ne, kuma ba za a amince da shi ta kowace hanya ba a aikin Yan sanda, don haka mun yaba da damuwar ’yan Najeriya masu kishin kasa da kungiyoyin da suka tura mana bidiyon. Za mu ci gaba da karbuwa da rungumar sabbin abubuwa da ra'ayoyin da za su iya haifar da sauyi ga 'yan sanda," in ji shi.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI