Akalla mutane uku ne suka mutu a wani rikicin kabilanci da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Gbagyi da Hausawa a titin 3rd Avenue Gwarinpa, Abuja.
An fara rikicin ne a ranar Asabar, 22 ga Afrilu, kuma ya kai kololuwa a ranar Litinin, 24 ga Afrilu.
A cewar Abuja Facts, fadan ya fara ne tsakanin direbobin Keke wadanda galibinsu Hausawa ne da kuma ‘yan kabilar Gbagi.
"Rahotanni sun nuna cewa an samu tashin hankali a titin 3rd Avenue Gwarinpa, saboda rikicin baya-bayan nan tsakanin Hausawa da 'yan kabilar Gbagyi," Abuja Facts ta rubuta a shafinta na Twitter yayin da take raba bidiyon da lamarin ya faru.
Wani faifan bidiyo da aka yada ta yanar gizo ya nuna wani mutum da jini na fitowa daga raunuka a fuskarsa.
A cikin faifan bidiyon an ji wata murya tana cewa wasu Hausawa masu sayar da kwayoyi da Keke a Gwarimpa, sun shiga gidan wani mashawarci domin yin fashi don haka ‘yan kabilar Gbayi suka fusata suka fito da daddare, inda suka nemi Hausawa su bar Gwarimpa.
Hakan ya haifar da arangama tsakanin bangarorin biyu har ta koma tashin hankali.
Mutane sun jikkata wasu kuma cikin bakin ciki sun mutu sakamakon raunukan da suka samu. An kuma lalata motoci a rikicin.
Sojoji sun shiga tsakani suka maido da zaman lafiya. Sai dai bayan tafiyar sojojin, rikicin ya ci gaba da faruwa a daren ranar Asabar, inda aka sake komawa da safiyar Litinin.
Viewers Discretion Is Advised⚠️
— ABUJA FACTS (@Abuja_Facts) April 23, 2023
Last night at Gwarinpa 3rd Avenue at about 9:30pm, a reported clash occurred between the keke napep riders and the indigenous Gbagy residents, which resulted into the death of 3 people, some people injured and over 30 cars vandalized. pic.twitter.com/IMj2fPoi9t
BY ISYAKU.COM