Wani malami a Sashen Biology na Kwalejin Ilimi ta Umar Suleiman Gashua, Jihar Yobe, Dokta Barde Luka Yelwa da matarsa, Godiya, sun rasu kwana biyu tsakani.
Dokta Yelwa, mai shekaru 38, ya rasu ne a ranar Alhamis, 20 ga Afrilu, 2023, bayan ya yi fama da ciwon zuciya a asibitin da yake jinyar matarsa da ta yi rashin lafiya.
Kwanaki biyu da rasuwarsa, daidai ranar Asabar, 22 ga Afrilu, matarsa ma ta rasu.
Ma’auratan sun bar ‘ya’ya biyu, yarinya ‘yar shekara 5 da yaro dan shekara 2.
Dr. Yelwa ya samu digirin digirgir (Ph.D). makonni biyu da suka gabata.
An sake dage jana’izar marigayi Dr. & Mrs Barde Luka Yelwa a ranar Litinin 24 ga Afrilu, 2023, kuma za a yi jana’izar marigayin ne a kauyen Dagare mai nisan kilomita 10 daga hanyar Bauchi zuwa Jos.
A halin da ake ciki, 'yan uwa da abokan aiki sun yi amfani da shafukan sada zumunta don jimamin ma'auratan.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI