Kuma dai: Lauya ya sake garzayawa Kotu neman kada a rantsar da Tinubu


Wani lauya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na Hope Democratic Party a 2019, Ambrose Owuru ya garzaya kotun daukaka kara yana neman ta dakatar da rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu.

 Lauyan, a kara mai lamba CA/CV/259/2023, ya bukaci kotun da ta dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga rantsar da zababben shugaban kasa na 2023 a watan Mayu.  29. PM News ya rahoto.

 Owuru ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019 kuma bai shafe wa'adin sa ba kamar yadda doka ta tanada.

 Ya kara da cewa tun 2019 Buhari ya ke kwace mulki saboda kotun koli ba ta tantance karar da ya shigar a 2019 ba inda ya kalubalanci nasarar Buhari.

 Oworu ya roki kotu da ta ba da umarnin cewa kada gwamnatin Buhari ta rantsar da Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023 har sai Kotu ta ci wa matsaya kan karar da ya shigar kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN