Bidiyon wani hijabi wanda mata suke sanyawa da aka masa farashina N1.8m ($4,500), ya janyo cece-kuce a soshiyal midiya.
Bidiyon wanda ya janyo mutane suka yi ta maganganun barkwanci a kansa da cacccakar tsadar da hijabin ya yi, ya nuna hijabin luntsume da ƙwalliya mai ƙayatarwa. Legit ya rahoto.
Wani shafin da ake sayar da kaya ne mai suna @7sisters_veils ya sanya bidiyon a manhajar Instagram.
Shafin ya yi ƙorafin cewa mutane sun dame su da ƙorafi akan kuɗin hijabin.
Wani shafin da ake sayar da kaya ne mai suna @7sisters_veils ya sanya bidiyon a manhajar Instagram.
Latsa nan ka kalli bidiyon
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI