Auren nasu na shekaru 22 ya ruguje a jihar Ekiti bayan da wani Boka ya mutu a saman matar Faston a lokacin da suke lalata a otal.
A cewar P.M.EXPRESS, Fasto Joshua ya bayyana cewa an raba auren sa ne a kotun al’ada ta jihar Ekiti bayan ya shigar da karar saki yana neman a raba auren da Rita bisa dalilin tana aikata zina.
Mai shigar da kara, Fasto Ajagunigbala, a yayin zaman kotun ya roki kotun da ta ruguza auren bisa laifin zina, kuma a ba shi izinin rikon ‘ya’yansa.
A wata shaida, ya gaya wa Kotun cewa bai biya sadakin wanda ake kara ba, kuma sun shafe sama da shekaru 22 suna zaune tare kuma suna da ‘ya’ya.
Ya kuma shaida wa Kotun cewa wannan shi ne karo na uku da ya kai ta kotu bisa laifin yin zina, inda ya bayyana cewa wanda ake kara tun a shekarar 2017 ta fara yin lalata da wani Boka mai suna Ifidayomi aka Ejiogbe.
Ya bayyana cewa Bokan, ya mutu ne a saman wanda ake kara yayin da yake jima'i a wani otal a Ikere-Ekiti a ranar 2 ga Janairu, 2023, wanda ya haifar da hargitsi kuma ya sanya ’yan daba suka lalata gidansa da cocinsa a garin Ikere.
Ya koka da cewa matakin da ta dauka ya sa hukumar ta Cocin ta dakatar da shi kuma saboda haka ya daina sha’awar ci gaba da rayuwa da ita inda ya roki Kotun da ta raba aurensu ta kuma ba shi kulawar ‘ya’yansa.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI