Type Here to Get Search Results !

Bayan mulki: Zan koma Nijar da zama idan...Buhari ya yi maganar da zai baka mamaki


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake ya koma kasar Jamhuriyar Nijar da zama idan ya sauka daga mulki.

Buhari ya sanar a ranar Karamar Sallah cewa ya kosa ya bar mulki ya koma mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

“Dauran ma, idan na koma can suka dame ni, to zan tsallaka in koma kasar Nijar,” in ji shi.

Ya ce tuni ya riga ya hada kayansa domin kuwa, ya kudirin aniyar zama nesa da Abuja idan ya sauka daga mulki.

Buhari wanda ya jima da cewa ya kosa ya bar mulki ya ce komawarsa Daura zai sama mishi isasshen hutu nesa da Abuja, bayan shekarun da ya yi a bisa mulki.

Hakan kuma, a cewarsa, zai kuma ba wa shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, damar yanke shawara da gudanar da mulkinsa yadda yake so.

Buhari ya kuma yaba wa ’yan Najeriya bisa hakurinsu da kamun ludayin gwamnatinsa na tsawon shekaru takwas.

Ya kara da cewa ya dauki laifin duk wani laifi ko caccaka ko zargin da ake wa gwamnatinsa, saboda shugabanci ya gaji haka.

Sannan ya roki ’yan kasar da su yafe masa duk abin da ya yi musu ba daidai ba a tsawon shekarun mulkinsa.

Da yake karbar bakuncin mazauna birnin tarayya da suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, Buhari ya ce shirme ne yadda ’yan siyasa suka rika amfani da bambancin addini da kabilanci a matsayin makaman siyasa a zaben da ya gabata.

Ya ba da misali da cewa a duk shari’o’in da ya shigar Musulmai ’yan Arewa shugabannin Kotun Koli a lokacin, amma hakan bai sa ya yi nasara a kotu ba.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN