An kashe wani dattijo tare da jikkata wasu da dama a wani rikicin sarauta a Karamar Hukumar Bogoro ta Jihar Bauchi. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
’Yan sanda sun ce kuma kona gidaje akalla 64 a rikicin da ya taso a daren Asabar a kan nadin basaraken kauyen Sang da ke karamar hukumar.
Kakakin ’yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Alkali, ya ce, “Wasu matasa daga bangarori daban-daban da ke adawa da nadin basaraken kauyen ne suka yi ta kai wa jama’a hari, suka kona gidaje 64 da babura uku da kuma kadarori na miliyoyin kudi.”
Ya ce an kashe wani dattijo mai shekara 70 mai suna Apollos Danlami, aka jikkata wani dan shekara 65 mai suna Naemiya Bature da kuma wasu da dama a hatsaniyar.
Sai dai ya ce bayan samun kiran gaggawa, ’yan sanda sun kai dauki zuwa kauyen domin tabbatar da doka da oda kuma zuwa yanzu kurar ta lafa.
A cewarsa, rundunar ’yan sandan jihar dauki matakan tabbatar da tsaro a karamar hukumar kuma Kwamishinan ’yan sandan jihar ya umarci DPO na Bogoro ya gudanar da cikakken binciken kan musabbabin rikon.
Ya kara da cewa ana kuma ci gaba da bincike domin cafke wadanda ke da hannu a rikicin domin su fuskanci hukunci.
BY ISYAKU.COM