Badakalar Kudi: Rarara Ya Nemi Kotun Shari'ar Musulinci Tayi Watsi Da Karar Da Ake Masa, Ya Bayar Da Dalilin Sa


Shahararren mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, ya buƙaci wata kotun shari'ar musulunci mai zama a jihar Kano, da ta yi fatali da ƙarar sa da aka shigar a gaban ta. Legit Hausa ya wallafa.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ana tuhumar Rarara da ƙin biyan wani ɗan kasuwa mai suna Muhammad Ma'aji, kuɗaɗen sa da yawan su ya kai sama da N10m.

Tun da farkon fara shari'ar mawaƙin bai samu halartar sauraron ƙarar da ake masa ba, cewar rahoton Daylight reporters

A yayin zaman kotun da aka ci gaba a Rijiyar Zaki, wacce mai shari'a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ke jagoranta, lauyan da ke kare Rarara, G. A. Badawi, ya gaya wa kotun cewa ƙarar ba ta da tushe ballantana makama saboda haka yakamata ayi fatali da ita.

Ya ƙara da cewa sun mayar da martanin su a rubuce kan ƙorafin da kotun, amma masu shigar da ƙara sai suka ce sun ga martanin a ƙurarren lokaci yayin da kotun ke shirin fara zaman ta.

Mai shigar da ƙorafin, Muhammad Ma'aji, ya gayawa kotun cewa yana da dukkanin hujjojin sa a rubuce waɗanda za su tabbatar da zargin da yake cewa tun lokacin da suka fara harƙallar kasuwanci da Rarara a shekarar 2021, bai bashi ko sisi ba.

Mai shari'a Halhalatul Khuza’i Zakariyya ya umurci lauyoyi masu shigar da mayar da martanin su a rubuce ga lauyoyi masu kare wanda ake ƙara da kuma kotun.

Mai shari'a Zakariyya ya ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 12 ga watan Mayun, 2023 domin cigaba da sauraron ɓangarorin biyu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN